ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press ya bayyana cewa ma’aikatar ta bada rahoton mutuwar mutane 117 sanadiyyar cutar a jiya jumma, wanda shi ne adadin da ya haura 100 a karon farko cikin watannin da suka gabata.
A halin yanzu dai jimillar mutane 62,876 suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar tun bayan bullarta a farkon shekara ta 2020 a kasar. Sima Sadat Lari kakkain ma’aikatar kiwon lafiyar ta kasa ta bayyana cewa mutane 11,660 ne suka kamu da cutar a jiya jumma’a kadai, sannan 1,330 daga cikinsu suna jinya a asbitocin kasar.Ya zuwa yanzu dai jimillar mutane 1,908,974 suka kamu da cutar sannan 1,633,949 suka warke.
342/